Isa ga babban shafi
FIFA

Kotu ta yi watsi da karar 'yan kwadago kan hukumar FIFA

Wata Kotu da ke zamanta a kasar Switzerland ta yi watsi da karar da wasu kungiyoyin kwadago suka shigar gabanta don neman ta karbar musu hakkinsu daga hukumar kula kwallon kafa ta duniya FIFA.

Babban filin wasan kwallon kafa na Khalifa da ke Qatar
Babban filin wasan kwallon kafa na Khalifa da ke Qatar
Talla

Kungiyoyin da suka fito daga kasashen Netherlands da Bangladesh, sun shigar da karar ce, bisa neman hakkinsu na rashin biyan cikakken albashi, da gwamnatin kasar Qatar ke yi, wadda zata karbi bakuncin gasar cin kofin duniya a shekara ta 2022.

To sai dai kotun ta yi watsi da bukatar saboda rashin samar da gamsassun hujjoji.

Da fari kungiyoyin kwadagon sun ruga kotu ne bayanda kungiyoyin kare hakkin dan’adam suka zargi gwamnatin Qatar da take hakkin ma’aikata akalla 5000 da ke ayyukan ginin filayen wasanni a kasar, da zasu karbi bakuncin gasar cin kofin duniya.

 

A watan Maris din da ya gabata, kungiyar kare hakkin dan’adam ta Amnesty International, wallafa rahoton cewa an yiwa ma’aikatan da ke aikin kwaskwarimar ginin babban filin wasan Qatar na Khalilfa, yawanci daga kasashen India, Bangladesh, da kuma Nepal karya, game yawan albashin da aka yi alkawarin za'a rika biyansu.

Batun zargin tauye hakkin ma’aikata dai na daya daga cikin bututuwan da ke cigaba da haifar da muhawara tun bayan bawa kasar Qatar damar karbar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a shekara ta 2022.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.