Isa ga babban shafi
Wasanni

Amunike na neman aikin horar da Zamalek

Tsohon dan wasan Najeriya Emmanuel Amunike na neman aikin horar da kungiyar Zamalek ta Masar.

Emmanuel Amunike
Emmanuel Amunike http://guardian.ng/sport
Talla

Amunike dai ya shafe kusan daukancin rayuwarsa ta kwallon kafa ya na buga wa kungiyar ta Zamalek tamaula, in da ya lashe mata kofunan gasar League ta Masar guda biyu.

Tun bayan da kungiyar ta sha kashi da ci 2-0 a gida a fafatawar da ta yi da Al Ahly a makon jiya, Zamalek ke neman kwararren kocin da zai ci gaba da horar da ‘yan wasanta.

Shugaban kungiyar Mortada Mansour ya tabbatar cewa, Amunike na cikin jerin mutanen da  suka gabatar da takardunsu don neman aikin mai horar da kungiyar.

Amunike, wanda ke da shaidar horarwa ta Turai, ya lashe kofin duniya na 'yan kasa da shekaru 17 a Chile a shekarar 2015 a matsayinsa na mai horar da karamar kungiyar kwallon kafa ta Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.