Isa ga babban shafi
Wasanni

Albashin Messi zai zarce na duk wani dan kwallo

Shugabann kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Josep Maria Bartomeu ya bayyana cewa, kungiyar ta shirya don fara bai wa Lionel Messi albashin da ya zarce na kowani dan kwallon kafa a duniya.

Lionel Messi na Barcelona
Lionel Messi na Barcelona LLUIS GENE / AFP
Talla

Shugaban ya ce, za su yi haka don ganin Messi ya ci gaba da taka leda a Barcelona har iya rayuwarsa ta kwallon kafa.

Sai dai Bartomeu bai sanar da adadin kudin da za a ci gaba da biyan gwarzon dan wasan ba da ya lashe kyautar kwallon zinari sau biyar da ake bai wa fiitaccen dan wasan shekara.

A shekarar 2018 ne kwantiragin Messi na yanzu zai kare.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.