Isa ga babban shafi
Wasanni

Arsenal ta gaza darewa teburin Premier

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta barar da damarta ta hayewa saman teburin gasar Premier ta Ingila sakamakon kashin da ta sha ci 2-1 a hannun Everton a wasan da suka yi jiya.

Kocin Arsenal Arsene Wenger
Kocin Arsenal Arsene Wenger Reuters/Matthew Childs
Talla

Arsenal ce ta fara zura kwallo a ragar Everton ta hannun Alexis Sanchez a minti na 20 da saka wasa, amma daga bisani Seamus Coleman ya farke wa Everton a minti na 44.

Sai kuma Ashley Williams da ya jefa kwallon karshe a minti na 86 ana dab da tashi wasan.

Yanzu haka dai Chelsea ce ke ci gaba da jan ragama a teburin gasar da maki 37, in da ta bai wa Arsenal tazarar maki uku.

Ita kuwa Everton na matsayi na bakwai da maki 23, yayin da a karo na farko kenan da ta samu nasara tun watan Octoban da ya wuce.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.