Isa ga babban shafi
Wasanni

An kwace kyautar 'yan wasan Olympics 10

Kwamitin shirya wasanni Olympics na Duniya IOC ya dauki matakin kwace lambobin yabo da ya karrama ‘yan wasa 10 da suka yi fice a wasannin Olympics da aka yi a shekara ta 2008. 

REUTERS
Talla

An kwace wadannan lambobin yabo ne sakamakon samun ‘yan wasan da laifin shan kwayoyin karin kuzari, bayan sake gudanar da gwajin tantance shan kwayoyi kan ‘yan wasan da suka fito daga kasashen Rasha da Ukraine.

Cikinsu dai babu mai lambar zinare sai dai lambobin Azurfa da kuma Tagulla.

Matakin sake bincikar ‘yan wasan da suka fafata a wasannin Olympics da aka yi a Beijing a 2008 da kuma wadda ta gudana birnin London a 2012, ya sa an samu jimillar ‘yan wasan motsa jikin da suka ga ta leko ta koma, bayan kwace lambobin yabon da suka lashe, yawansu ya kai, 76.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.