Isa ga babban shafi
FIFA

FIFA zata yaki cin hanci da rashawa

Hukumar Kula da kwallon kafa ta Duniya FIFA, ta ce zata dauki tsattsauran mataki na dakatar tallafin kudi ga hukumomin kula da kwallon kafa da ke kasashe Duniya, muddin suka gaza daukar matakan yaki da cin hanci da rashawa.

Shugaban FIFA Gianni Infantino
Shugaban FIFA Gianni Infantino REUTERS/Jorge Adorno
Talla

Shugaban FIFA Gianni Infantino ya ce, yanzu haka ya sawa ilahirin hukumomin na kasashe daban daban har 211 dake karkashin FIFA ido don ganin sun gudanar da ayyukansu kamar yadda doka ta tsara, ba tare da sanya siyasa a harkar wasanni ba.

Tuni FIFA ta kafa wasu karfafan kwamitoci 11 da zasu gudanar da aikin bin diddigin yaki da cin hanci da rashawa tsakanin hukumomin kula da kwallon kafa 211 da ake da su.

Tun bayan zabar Infantino a mtasayin Shugaban FIFA, ya sha alwashin kawo karshen batun cin hanci da rashawa a tsakanin jami’an FIFA domin dawo da martabar hukumar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.