Isa ga babban shafi
Wasanni

Bale zai ci gaba da zama a Real Madrid

Wani lokaci a yau ne dan wasan Real Madrid Gareth Bale zai gana da ‘yan jaridu bayan da kungiyar ta tsawaita kwantiragin da zai ba shi damar ci gaba da murza a leda Santiago Bernabeu har zuwa shekarar 2022.

Gareth Bale na Real Madrid
Gareth Bale na Real Madrid Reuters / Carl Recine
Talla

A shekarar 2013 ne, Bale mai shekaru 27 ya koma Real Madrid daga Tottenham akan kwantiragin shekaru shida, in da a wancan lokacin aka siye shi akan Pam miliyan 85.

Sannan kuma ya taimaka wa Madrid lashe kofuna biyar a gasa daban-daban da suka hada da gasar cin kofin zakarun Turai, yayin da kuma ya ci mata kwallaye 62 a wasannin 135 da ya buga mata.

Rahotanni sun ce, dan wasan na karban pam dubu dari 600 a kowani mako amma ya na tashi da pam dubu 350 bayan an cire haraji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.