Isa ga babban shafi
Spain

Barcelona ta kai karar shugaban La Liga

Kungiyar Barcelona ta kai karar shugaban wasannin gasar La liga Javier Tebas a babbar kotun wasanni ta Spain bayan ya soki ‘yan wasan kungiyar kan abinda ya biyo bayan wasansu da Valencia.

'Yan wasan Barcelona Suárez da Neymar da Messi
'Yan wasan Barcelona Suárez da Neymar da Messi REUTERS/Albert Gea
Talla

Barcelona dai ta sha da kyar ne a hannun Valencia 3-2.

Magoya bayan Valencia kuma sun jefi Neymar da Messi da Suarez ne da robar ruwa yayin da suke murnar kwallon da Messi ya zira a bugun fanariti a lokacin da ya rage dakikoki a hure wasan.

Shugaban La liga kuma ya ce ‘yan wasan Barcelona ne suka takali magoya bayan Valencia, saboda yadda suka je gabansu suna murna.

Wannan ne dai ya fusata Barcelona har ta kai karar shugaban na La liga.

Hukumar kwallon Spain ta ci tarar Valencia kudi euro 1,500 tare da yin gargadi ga kungiyar akan ana iya daukar matakin rufe filin wasanta idan haka ta sake faruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.