Isa ga babban shafi
Wasanni

Real Madrid ta dare saman teburin La Liga

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta dare saman teburin gasar La Liga bayan da ta yi nasarar casa Atletico Bilbao da ci 2-1 a karawar da suka yi jiya Lahadi.

Cristiano Ronaldo da Gareth Bale  na Real Madrid
Cristiano Ronaldo da Gareth Bale na Real Madrid REUTERS/Kai Pfaffenbach
Talla

Karim Benzema ne ya fara jefa kwallon farko a ragar Atletico Bilbao a minti na 7 da fara wasan kafin daga bisani Merino ya farke wa Atletico Bilbao a minti na 27.

Sai dai ana gab da tashi wasan ne, Morata ya jefa kwallon da ta bai wa Madrid nasara.

Christiano Ronaldo dai ya zubar da damar da ya samu na zura kwallaye, in da ya kai hari har sau 11 amma biyu kadai ne daga ciki suka nufi mai tsaren ragar Bilbao.
 

A bangare guda, Lionel Messi na Barcelona ya ci wa kungiyarsa kwallaye 2 a fafatawar da suka tashi 3-2 da Valencia a gasar ta La Liga, in da Luis Suarez da ya lashe kyautar takalmin zinari ya ci wa Barcelona kwallo ta uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.