Isa ga babban shafi
Wasanni

Chelsea ta lallasa Manchester United da ci 4-0

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta lallasa Manchester United da ci 4-0 a karawar da suka yi a jiya a gasar premier ta Ingila.

Marcos Alonso ina Chelsea a yayin fafatawa da Manchester United a Stamford Bridge a gasar Premier ta Ingila
Marcos Alonso ina Chelsea a yayin fafatawa da Manchester United a Stamford Bridge a gasar Premier ta Ingila Reuters/John Sibley
Talla

Ana iya cewa, Mourinho ya sha kashi a hannun tsoffin yaransa a Stamford Bridge, in da bayan bude wasan da kasa da minti guda, Pedro ya jefa kwallon farko a ragar Manchester United.

Wannan nasarar ta bai wa Chelsea damar darewa saman Tottenham, in da a yanzu take a matsayi na hudu kuma banbancin maki daya ne tsakaninta da Manchester City da Arsenal da Liverpool da ke gabanta.

A karon farko kenan da Mourinho ya kai ziyara Stamford Bridge tun bayan da Chelsea ta sallame shi a cikin watan Disamban bara bayan kungiyar ta gaza kai wa ga gaci a gasar Premier bara.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.