Isa ga babban shafi
Wasanni

Celtic da Manchester City sun tashi ci 3-3

Celtic da Manchester City sun tashi ci 3-3 a gasar cin kofin zakarun Turai, wasan da ya bai wa Celtic daga rukunni C damar samun makinta na farko.

Kocin Manchester City Pep Guardiola
Kocin Manchester City Pep Guardiola Reuters/Lukas Barth
Talla

Da farkon soma wannan wasa Celtic ke kan gaba da yawan kwallaye kafin daga bisani City ta farke har suka kai ga tashi da ci 3-3.

Kocin Manchester City Pep Guardiola da ke bayyana rashin jindadinsa da wasan da ya ke gani ya kamata su yi Nasara, Ya ce a yanzu ‘yan wasansa za su koyi darasi da alfannu soma wasa mai kyau.

Ita kuwa Barcelona ta doke Monchengladbach ne da ci 2-1, Nasara da ya ba ta damar dare zaman teburin su na C, yayin da city ke mataki na 2 da banbanci maki 2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.