Isa ga babban shafi
Wasanni

Allardyce ya rasa kujerarsa ta kocin Ingila

Aikin Sam Allardyce a matsayin kocin tawagar kwallon kafar Ingila ya kawo karshe a yau, bayan ya jagorance ta na tsawon kwanaki 67.

Kocin Ingila Sam Allardyce
Kocin Ingila Sam Allardyce Reuters/Russell Cheyne
Talla

Wannan kuma na zuwa ne bayan jaridar Daily Telegraph ta wallafa wasu zarge-zarge a kansa.

Binciken da jaridar ta gudanar ya nuna cewa, Allardyce mai shekaru 61 ya amince ya karbi wata harkar da za ta ba shi Pam dubu 400 a ganawar da ya yi da ma'aikatan jaridar da suka boye kansu a matsayin 'yan jarida, in da suka gabatar daa kansu a matsayin 'yan kasuwa.

'Yan jaridan da suka nadi kalaman Allardyce a sirce, sun jarraba shi, in da suka bukaci ya kasance wakilinsu a wani kamfani a Singapore da Hong Kong kuma ya amince da haka.

A cikin tattaunawar da suka yi, har ila yau, Allardyce ya yi katobara, in da ya bayyana cewa, za a iya  kauce wa dokokin kasuwar cinikayyar ‘yan wasa. 

Har ila yau an zargi kocin da caccakar hukumar kwallon kafar Ingila har ma da wanda ya gada wato Roy Hodgson.

Tuni dai hukuamar kwallon kafar kasar ta bayyana wannan dabi’ar ta Allardyce  a matsayin abin kyama kuma a halin yanzu Gareth Southgate ne zai maye gurbinsa a matsayin kocin rikon kwarya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.