Isa ga babban shafi
Wasanni

Real Madrid ta kafa tarihi a La Liga

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta kafa tarih a gasar La Liga, in da ta samu nasara a wasanni 16 a jere bayan da ta doke Espanyol da ci 2-0 a jiya Lahadi.

Real Madrid ta kafa tarihi a gasar  La Liga, in da ta samu nasara sau 16 a jere
Real Madrid ta kafa tarihi a gasar La Liga, in da ta samu nasara sau 16 a jere
Talla

A karon farko kenan cikin watanni biyar da James Rodriguez ya ci wa Real Madrid kwallo a fafatawar ta jiya gabanin tafiya hutun rabin lokaci, yayin da Karim Benzema shi ma ya zura tasa a minti na 70 da fara wasa.

Real Madrid ta yi wasan jiya ne ba tare da zaratanta ba wato, Christiano Roanldo da Gareth Bale.

Bacelona ce dai ta fara kafa wannan tarihin na samun nasara sau 16 a jere a kakar 2010-2011 kuma a karkashin jagorancin Pep Guadiola.

Yanzu haka dai, Real Madrid ce ke kan jan ragama a taburin La Liga da maki 12, in da ta bai wa Barcelona da Las Palmas tazarar maki uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.