An kammala gasar nakasassu a birnin Rio
A jiya Lahadi aka rufe gasar nakasassu ta Paralympics da birnin Rio na Brazil ya dauki nauyin gudanarwa, in da aka cashe da wake-wake da raye-raye a filin wasa na Maracana .
Wallafawa ranar:
Sannan kuma an gudanar da wasan wuta a yayin da nakasassun ‘yan wasan ke zaune a filin na Maracana.
Daga cikin mawakan da suka nishadantar da jama’a akwai, Jonathan Bastos wanda aka haife shi da nakasa a Brazil amma ya zama fitaccen mawaki a kasar, kuma ya kan kada jita da ‘yan yatsun kafafunsa.
Najeriya dai ta yi abin-azo-a-gani a gasar, in da ta lashe lambobin yabo 12 da suka hada da zinari 8 da azurfa 2 da tagulla 2, kuma ita ce ta ja ragama a Afrika, yayin da Tunisiya da Afrika ta Kudu ke bi mata.
Nakasassun ‘yan wasan na Najeriya sun samu kyakkyawar tarba daga ‘yan kasar bayan sun sauka a filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke birnin Abuja.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu