Isa ga babban shafi
Wasanni

Djokovic ya soma US Open da kafar dama

Zakaran Tennis a duniya Novak Djokovic ya soma gasar US Open da kafar dama, inda ya doke Jerzy Janowicz na Poland duk da raunin da Djokovic na Serbia ke fama dashi a hannu.

Novak Djokovic ya soma gasar US Open da kafar dama
Novak Djokovic ya soma gasar US Open da kafar dama RFI/Pierre René-Worms
Talla

Djokovic ya doke Jerzy ne da ci 6-3, 5-7, 6-2, 6-1.

Shima Rafael Nadal na Spaniya ya ci wasansa daya fafata da Denis Istomin na Uzbekistan da ci 6-1, 6-4,6-2.

Nadal dai bai haska a gasar French Open da Wimbledon ba saboda raunin da yayi ta fama dashi a hannu, inda ya ce wannan shekarar bata zo masa cikin sauki ba.

Yayin da a fanin Mata Angelique Kerber ta doke Hercog ta Poland da ci 6-0,1-0.

Garbine Muguruza ta Spain tayi kokari cinye Elise Mertens ta Belgium da ci 2-6, 6-0, 6-3.

Ita kuma zakaran Olympic Monica Ping an doke ta a wasanta na farko, inda Zheng Saisai ta China ta mata ci 6-4, 6-2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.