Isa ga babban shafi
Olympics

Rio: Bolt ya lashe Zinari a tseren gudun mita 200

Dan tseren gudun Jamaica Usain Bolt ya sake lashe zinari a tseren gudun mita 200 a jiya Alhamis cikin dakika 19 a wasannin Olympics da ake gudanarwa a birnin Rio na Brazil bayan ya lashe zinari a tseren gudun mita 100.

Dan gudun Famfalaki Usain Bolt
Dan gudun Famfalaki Usain Bolt REUTERS/Lucy Nicholson
Talla

A yau juma’a kuma Bolt na harin sake lashe zinari a tseren gudun mita 400 amma na karbar tuta tsakanin ‘Yan tseren gudu 4.

Bayan lashe zinarin a jiya Bolt ya ce hakan ke tabbatarwa duniya da cewa babu wani kamar shi a gudun famfalaki.

Tuni dai Bolt ya ce wannan ne karo na karshe da zai haska a wasannin Olympics.

Dan tseren gudun na Jamaica ya taba lashe zinari sau uku a wasannin da aka gudanar a 2008 da kuma 2012.

Dan tseren gudun Canada ne Andre de Grasse ya lashe Azurfa a tsereen gudun na mita 200 cikin dakika 20 yayin da dan tseren gudun Faransa Christophe Lemaitre ya lashe tagulla a matsayi na uku.

A yau juma’a akwai tsreen gudun mita 5,000 zagayen karshe

Haka ma akwai tsaren tafiya kilomita 50 a bangaren maza. A bangaren mata ma akwai tseren tafiyar na kilomita 20.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.