Isa ga babban shafi
Spain

Barcelona ta lashe Super Cup na Spain

Barcelona ta lashe Super Cup na Spain bayan ta casa Sevilla da jimillar kwallaye ci 5-0. A jiya Barcelona ta doke Sevilla ne 3-0 bayan a karawa ta farko ta doke ta ci 2-0.

Barcelona ta lashe Super Cup karo na 12 bayan ta doke Sevilla
Barcelona ta lashe Super Cup karo na 12 bayan ta doke Sevilla REUTERS
Talla

Karo na 12 ke nan da Barcelona ke lashe kofin kuma kofi na 10 ke nan da Luis Enrique ke dauka a matsayin kocin kungiyar.

Ana fafatawar lashe Super Cup ne tsakanin kungiyar da ta lashe La liga da kuma kungiyar da ta lashe Copa Del Ray. Kuma Barcelona ce ta lashe kofunan biyu a kakar da ta gabata, amma da Sevilla ta buga wasan karshe a Copa del Ray.

Arda Turan da Lionell Messi ne suka jefa wa Barcelona kwallayenta a ragar Sevilla.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.