Isa ga babban shafi
kwallon kafa

Pogba na dab da zama dan Wasan Manchester

Rahotanni sun ce nan da sa’o’I 48 kungiyoyin Manchester United da Juventus za su kawo karshen akan cinikin dan wasan Faransa Paul Pogba akan kudi euro miliyan 110.

Paul Pogba zai kasance dan wasa mafi tsada a duniya
Paul Pogba zai kasance dan wasa mafi tsada a duniya Reuters
Talla

Jaridun Italiya sun ce Manchester za ta amince da farashin da Juventus ta aza akan Pogba wanda kyauta Man U ta saki dan wasan a 2012.

Idan dai har haka ta tababbata Pogba zai kasance tsadadden dan wasa a duniya.

Kafar wasanni ta Sky Sport a Italiya ta ce daga nan zuwa gobe Juma’a ana iya kawo karshen cinikin.

Amma wasu jaridun Birtaniya tuni suka ruwaito cewa cinikin ya kankama, kuma Man U ta amince ta biya dan wasan kudi fam dubu ashirin da biyar duk mako.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.