Isa ga babban shafi
Wasanni

An haramta wa Rasha shiga wasannin Olympics

Kotun ladabtar da ‘yan wasa ta goyi bayan hukuncin dakatar da ‘yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na Rasha daga shiga wasannin Olympics a Rio na Brazil.

Kotu ta goyi bayan haramta wa 'yan wasan Rasha shiga wasannin Olympics na Brazil
Kotu ta goyi bayan haramta wa 'yan wasan Rasha shiga wasannin Olympics na Brazil REUTERS/Ueslei Marcelino
Talla

Hukumar kula da wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya ce ta haramta wa ‘yan wasan Rasha shiga wasannin da za a fara a ranar 5 ga watan gobe.

Hukumar ta IAAF ta dauki matakin ne bayan wani rahoto ya bayyana yadda ‘yan wasan ke kwan-kwadan kwayoyin kara kuzari, lamarin da ake zargin hannun gwamnati a ciki.

Kotun ta goyi bayan dakatarwar ce a wannan Alhamis bayan ‘yan wasan na Rasha sun shigar da kara kan hukuncin da IAAF ta dauka a kan su.

A bangare guda, shi ma kwamitin wasannin Olympic na duniya na nazari kan batun haramta wa ilahirin ‘yan wasan Rasha shiga wasannin Olympics a Brazil.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.