Isa ga babban shafi
Brazil

Yan Brazil na adawa da wasanni Olympics a kasar su

Wani Bincike da aka gudanar a kasar Brazil ya nuna cewar rabin al’ummar kasar basa bukatar ganin an gudanar da gasar wasannin Olympics da ake shirin farawa kasa da makwanni biyu masu zuwa.

Ana cigaba da shirye-shiryen wasanni Olympics a Brazil
Ana cigaba da shirye-shiryen wasanni Olympics a Brazil REUTERS/Sergio Moraes
Talla

Ra’ayin jama’ar da jaridar Folha ta wallafa ya nuna cewa, yawan yan kasar Brazil dake kin jinin gudanar da gasar ta Olympics sun rubanya tun bayan gudanar da makamacin sa a kasar shekaru uku da suka gabat.

Wasan Olympic na Rio de Janeiro, da za a fara a farkon watan Augustan gobe shine irinsa na farko da za ayi a wata kasa dake nahiyar Amurka ta kudu.

Kasar Brazil dake fama da matsalar koma bayan tattalin arziki irinsa mafi muni da tataba gani a cikin shekaru sama da 10 na fama da badakalar cin hanci da rashawa da ta shafi wasu manyan kusoshin siyasar kasar, da ta kai ga tsige shugabar kasar Dilma Rousseff daga kan mukaminta.

Kuri’ar jin ra’ayin jama’ar kan wasan na Olympics ta samu amincewar kashi 40 cikin 100 ne kacal na al’ummar kasar, sabanin kashi 64 cikin dari na al’umma da suka amince da ita sheakru 3 da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.