Isa ga babban shafi
Ingila

Allardyce zai zama kocin Ingila

Nan da sa’o’i 24 hukumar kwallon Ingila za ta tabbatar da kocin Sunderland Sam Allardyce a matsayin sabon mai horar da ‘yan wasan kasar.

Kocin Sunderland  Sam Allardyce
Kocin Sunderland Sam Allardyce Reuters/Russell Cheyne
Talla

Allardyce shi zai gaji Roy Hodgson wanda ya ajiye aikinsa bayan Iceland ta fitar da Ingila a gasar cin kofin Turai da aka kammala a Faransa.

Yanzu Allardyce zai bar Sunderland bayan shafe watanni 9 a matsayin kocin kungiyar.
Allerdyce mai shekaru 61 ya horar da kungiyoyin Bolton da Newcastle da West Ham kafin Sunderland.

Yanzu FA za ta sasanta da Sunderland akan yarjejeniyar shi da ba ta kawo karshe ba da kungiyar.

Sai dai wasu na ganin rashin horar da manyan kungiyoyin Ingila, Sam Allardyce ba shi ba ne zabin da ya dace da Ingila ba inda har yanzu kasar ke fadi tashi a gasar cin kofin duniya da kofin Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.