An daure Pistorius shekaru 6 a gidan kurkuku
Kotu a kasar Afirka ta Kudu ta yanke hukuncin dauri na tsawon shekaru shida a gidan yari akan Oscar Pistorius tsohon zakaran gudun nakasassu a duniya saboda kisan Reeva Steenkamp a 2013.
Wallafawa ranar:
An dai yankewa Pistrorius wannan hukunci ne sakamakon daukaka kara da dangin tsohuwar budurwarsa Reeva suka shigar, inda suke nuna rashin amincewarsu da hukuncin farko da aka yanke ma san a shekaru biya, wanda daga bisani aka ba shi damar ci gaba da rayuwa a gidansa.
A ranar farko ta fara wannan sabuwar shara’a, Pistorius ya cire kafafuwansa na karfe inda ya rika tafiya akan dungu, yana neman kotu ta yi ma sa sassauci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu