Isa ga babban shafi
Euro 2016

CONMEBOL na son ayi fafatawar Copa-Euro

Hukumar kwallon kafa ta kudancin Amurka ta bukaci Hukumar kwallon kafa ta Turai ta amince a fafata tsakanin kasar da ta lashe Copa America a bana da kuma kasar ta lashe kofin Euro na 2016.

Tambarin gasar cin kofin Turai da ake gudanarwa a Faransa
Tambarin gasar cin kofin Turai da ake gudanarwa a Faransa ®portal gda
Talla

Shugaban hukumar kwallon kudancin Amurka Alejandro Dominguez ne ya shaidawa manema labarai a yau.

Ya ce sun aika da bukatar buga wasan amma suna jiran amsa daga EUFA.

Hukumar kwallon CONMEBOL ta ce tana son a yi wasan ne domin bikin cika shekaru 100 da gasar Copa Amerika ta Centanario da ake bugawa a Amurka.

Wannan na zuwa ne a yayin da Chile da Argentina za su buga wasan karshe a ranar Lahadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.