Isa ga babban shafi
FIFA

Blatter da Valcke sun arzuta kansu a FIFA

Wani sakamakon bincike da aka fitar a hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ya bankado tsoffin jiga-jigan hukumar sun yi amfani da mukaminsu domin artzuta kansu.

An walakanta Sepp Blatter da kudi kan batun rashawa a FIFA
An walakanta Sepp Blatter da kudi kan batun rashawa a FIFA AFP
Talla

Binciken da aka fitar a yau Juma’a ya ce Tsohon shugaban hukumar FIFA Sepp Blatter da Sakatarensa Jerome Valcke da kuma daraktan kula da kudi na hukumar Markus Kattner sun kirkirowa kansu wasu kudaden lada da wasu kwangiloli na miliyoyin daloli domin arzuta kansu

Binciken ya ce mutanen uku sun tsara wa kansu Karin albashi duk shekara da wasu kudaden lada da ke fitowa daga gasar cin kofin duniya.

Binciken ya ce FIFA na samun kudi sama da dala Biliyan 5 tsakanin shekaru hudu da ake gudanar da gasar cin kofin duniya, kuma mutanen uku na ware wa kansu wani kaso daga cikin kudin.

Binciken ya ce mutanen uku sun samu kudi dala miliyan 80 a shekaru biyar.

Dukkaninsu dai an dakatar da su kuma suna fuskantar bincike a Switzerland da kuma Amurka.

Binciken dai yanzu ya dada fito da girman rashawa a FIFA.

Jim kadan bayan fitar da rahoton, rahotanni sun ce jami’an Switzerland sun kai samame ofishin FIFA a Zurich kuma sun kwashe takardu da dama.

Majiyoyi daga FIFA sun ce masu binciken a Switzerland sun kai farmakin ne ofishin daraktan kudi Markus Kattner a yau Juma’a.

Wata jaridar Jamus ta ruwaito cewa shi kan shi shugaban hukumar ta FIFA na yanzu Infantino yana fuskantar bincike kan wata badalaka na sabawa dabi’un FIFA.

Jaridar Die Welt ta ruwaito cewa sabon shugaban ya bayar da umurnin lalata takardar da aka rubuta bayanan da aka tattauna a zaman babban Taron FIFA a Mexico.

Kuma yanxu haka kwamitin da’a na FIFA ya kaddamar da bincike akan Infantino kuma akwai yiyuwar dakatar da shi na tsawon watanni 3 idan har an tabbatar da zargin da ake ma shi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.