Isa ga babban shafi
Wasanni

Andy Murray zai fafata da Croat Ivo Karlovic a Roland Garros

A yau Juma'a Andy Murray zai fafata da Croat Ivo Karlovic a Roland Garros zageye na Uku, bayan tsallake mataki na farko da na biyu a wasanni biyu masu zafi, na farkon gasar da ake gudanarwa a birnin Paris.

Andy Murray a Roland Garros ta shekarar 2016
Andy Murray a Roland Garros ta shekarar 2016 RFI/Pierre René-Worms
Talla

Murray ya shafe tsawon sa’o’I 7 da dakikoki 14, a karawarsu da Redek Stapanek da Mathias Bourgue kafin kaiwa wannan zagaye.

Murray zai hadu da Karlovic mai shekaru 37 wanda ya kasance mafi yawan shekaru dake kaiwa wannan zagaye, tun bayan Jimmy Connors a shekarar 1991, daya kai irin wannan zagaye a US Open.

Shima Aljaz Bedene na Britaniya zai fafata da zakaran Tennis a Duniya Novak Djokovic bayan doke Pablo Carreno Busta domin kaiwa zagaye na Uku, a karon farko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.