Isa ga babban shafi
Najeriya

An dakatar da Giwa FC a Firimiyar Najeriya

Hukumar kula da wasannin Firimiya lig a Najeriya ta dakatar da kungiyar Giwa FC daga wasannin gasar bayan kauracewa wasu wasanninta har karo uku.

A garin Jos ne Kungiyar Giwa ta ke a arewacin Najeriya
A garin Jos ne Kungiyar Giwa ta ke a arewacin Najeriya completesportsnigeria.com
Talla

Hukumar ta tabbatar da dakatar da Giwa FC ne a wasannin kakar bana a cikin wata sanarwa da ta fitar a Twitter.

Kungiyar mallakin Chris Giwa ne wanda ke hamayyar shugabancin hukumar kwallon kafa ta NFF.

Mista Giwa dai ya dage kan cewa shi ne zababben shugaban hukumar NFF, matakin da ya sa hukumar FIFA ta yi barazanar dakatar da Najeriya.

A makon jiya ne kuma NFF ta dakatar da Giwa tare da wasu magoya bayan shi na tsawon shekaru 5 bayan ya maka hukumar kotu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.