Isa ga babban shafi
Wasanni

Leicester City ta lallasa Swansea

Dan wasan gaba na Leicester city, Leonardo Ulloa ya jinjina wa tawagarsa bayan ta lallasa Swansea City da ci 4-0 a fafatawar da suka yi jiya a gasar Premier ta Ingila, lamarin da ya kara mata kawarin gwiwa a kokarin da ta ke yi don ganin ta lashe kofin Premier.

Leicester City na hankoron lashe kofin gasar Premier ta bana
Leicester City na hankoron lashe kofin gasar Premier ta bana Reuters / Eddie Keogh Livepic
Talla

Ulloa wanda ya maye gurbin Jamie Vardy a wasan na jiya ya zura kwallaye guda biyu yayin da Riyad Mahrez da Marc Albrighton dukkanin su suka ci wa Leicester kwallo guda- guda.

Jamie vardy bai buga wasan na jiya ba sakamakon haramta masa buga wasa bayan hukumar kwallon Ingila ta same shi da laifin nuna rashin da’a ga alkalin wasa Jon Moss wanda ya bashi jan kati a fafatawar da Leicester ta yi da Wset Ham amma Vardy ya yi ja- in-ja da alkalin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.