Isa ga babban shafi
Zakarun Turai

Barcelona ta doke Arsenal

Arsenal ta sha kashi a gidanta a hannun Barcelona ci 2 da 0 a gasar Zakarun Turai da suka fafata a London a daren jiya zagaye na biyu, yayin da kuma Juventus da Bayern Munich suka tashi ci 2 da 2 a Italiya.

Lionel Messi ya ci kwallaye biyu a ragar Arsenal
Lionel Messi ya ci kwallaye biyu a ragar Arsenal REUTERS
Talla

Lionel Messi ne ya jefa wa Barcelona kwallayenta biyu a ragar Arsenal bayan an dawo hutun rabin lokaci.

Kwallayen Messi biyu dai masu tsada ne da ya jefa a gidan Arsenal, kuma yanzu kungiyar na kofar ficewa gasar a karo na 6 a jere da jere a irin wannan zagaye na biyu.

Yanzu Barcelona ta buga wasanni 33 ba a samu galabarta ba a dukkanin wasanninta.

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya soki ‘yan wasan shi musamman yadda suka kasa kare gidansu tare da kasa rike Barcelona a Emirates.

Wenger yace da an tashi babu ci da ya fi jin dadi a wasan. Yanzu dai Arsenal ta kasance kungiya ta biyu a Ingila da ta sha kashi bayan PSG ta doke Chelsea ci 2-1.

A ranar 16 ga watan Maris Arsenal zata kai wa Barcelona ziyara a karawa ta biyu.

Juventus da Bayern Munich

Stefano Sturaro ya kwaci Juventus ne a hannun Bayern Munich wanda ya rama kwallo ta biyu da manyan kungiyoyin biyu suka tashi ci 2 da 2.

Dan wasan Bayern Munich Arjen Robben ya jefa kwallo a ragar Juventus.
Dan wasan Bayern Munich Arjen Robben ya jefa kwallo a ragar Juventus. REUTERS/Giorgio Perottino

 

Ana dab da zuwa hutun rabin lokaci Thomas Mueller ya fara bude ragar Juventus, bayan an dawo hutun rabin lokaci Arjen Robben ya jefa kwallo ta biyu. Amma ‘Yan wasan Juventus Sturaro da Dybala ne suka farke kwallayen.

Sakamakon wasan dai ya nuna dukkanin kungiyoyin biyu na da fatar kai wa zagayen kwata fainail sai dai Bayern Munich ta fi kwarin guiwa saboda kwallaye biyu da Juve ta bari aka jefa a ragarta a gida.

Juve dai na iya jefa kwallaye a ragar Bayern a haduwarsu a Allianz Arena.

Wasannin Laraba

A yau akwai ci gaba da wasannin na gasar zakarun Turai kuma Atletico Madrid ce za ta kai wa PSV Eindhoven ziyara

A Ukraine kuma Dynamo Kiev za ta karbi bakuncin Manchester City.

Cikin kungiyoyin Ingila da suka rage a gasar, wata kila Manchester City ta ba marar da kunya a yau, bayan an doke Chelsea da Arsenal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.