Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Manchester City ta kulla yarjejeniya da Guardiola

Manchester City ta tabbatar da Pep Guardiola na Bayern Munich a matsayin sabon kocinta idan an kammala kakar wasan bana. Kungiyar ta sanar a shafinta na intanet cewa Guardiola zai fara aiki daga ranar 30 ga watan Yuni.

Guardiola zai karbi aikin horar da Manchester City daga Manuel Pellegrini
Guardiola zai karbi aikin horar da Manchester City daga Manuel Pellegrini REUTERS
Talla

Tuni dai Tsohon kocin na Barcelona Pep Guardiola mai shekaru 44 ya sanar da zai koma gasar Firimiya Lig bayan tabbatar da zai bar Bayern Munich.

Rahotanni sun ce Guardiola ya amince ne da yarjejejeniyar shekaru uku da Manchester City. Kuma kimanin kudi yuro miliyan 20 kungiyar za ta biya shi duk shekara.

Sai dai kuma babbar bukatar City akan Kocin shi ne taimaka mata lashe kofin gasar zakatun Turai.

Manchester City dai ba ta taba tsallakawa zuwa zagayen kwata fainal ba a gasar zakarun Turai, kuma kasancewar kungiyar cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa shi ne babban kalubalen da ke gaban Guardiola idan har ya fara aikin horar da ‘yan wasanta.

Masharhanta dai musamman a jaridun Birtaniya na ganin Guardiola na iya karbo Messi daga Barcelona domin cim ma bukatun kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.