Isa ga babban shafi
wasanni

Messi ya lashe Ballon d'Or karo na biyar

Dan wasan Barcelona Lionel Messi na Argentina ya lashe gwarzon shekara na hukumar FIFA Ballon d’Or a karo na biyar, a takarar da suka tsaya tsakanin 'Yan wasan uku, da suka hada da Cristiano Ronaldo na Portugal da kuma Neymar na Brazil.

Issa Hayatou na FIFA da  Lionel Messi yayin karban kyautar sa ta Ballon d'Or.
Issa Hayatou na FIFA da Lionel Messi yayin karban kyautar sa ta Ballon d'Or. REUTERS/Ruben Sprich
Talla

Tun kafin sanar da wanda ya lashe wannan kambu, daman an ta hasashen Messi na Barcelona ne zai karbi kyautar karo na biyar fiye da abokin hamayyarsa Cristiano Ronaldo na Real Madrid wanda ya lashe kyautar a bara kuma karo na uku.

Messi ya yi wannan nasara ne bayan samun yawan kuri’u kashi 41.33 cikin 100, sama da Cristiano da ke da kashi 27.76 cikin 100, yayin da Neymar ya samu kashi 7.86 cikin 100.

Tsakanin shekarar 2009-2012 Messi ke lashe wannan kayutar a jere da jere, sannan ya jefa wa Barcelona kwallaye 48 a 2015.

Baya ga wannan kyautar, A bana Messi ya lashe kyautar gwarzon dan wasa a Spain, sannan ya karbi kyautar gwarzon dan wasa ta Globe Soccer Award a Dubai.

Jarumar Duniya

Carli Llyod ta Amurka ce ta lashe kyautar mata da ke taka kwallon kafa a duniya.

Inda ta doke Aya Mayama ta Japan da Celia Sasic ta Jamus.
 

Kocin shekarar

Kocin Barcelona Luiz Enrique ne ya lashe kambu, bayan samun yawan kuri’u kashi 31.08 cikin 100 sama da kocin Bayern Munich Pep Guardiola da ya samu 22.97 cikin 100 da kuma mai horar da ‘yan wasan kasar Chile Jorge Sampaoli na Argentina. 9.47 cikin 100.

Yayin da Jill Ellis ta Amurka, ta lashe kambun kociyar shekarar

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.