Isa ga babban shafi
Ballon d'Or

Messi da Ronaldo da Neymar ke takarar Ballon d’Or

Critiano Ronaldo da Lionel Messi da Neymar Jr. ke takarar FIFA Ballon d'Or, kyautar gwarzon dan wasan duniya na bana, wadanda FIFA ta bayyana a jiya Litinin.

Ronaldo, Messi, Neymar ke takarar gwarzon dan wasan duniya a bana
Ronaldo, Messi, Neymar ke takarar gwarzon dan wasan duniya a bana FIFA
Talla

Ronaldo na Real Madrid ne ke rike da kambun da ya lashe a bara, kuma karo na uku.

Messi kuma na harin lashe kyautar ne karo na biyar. Wannan ne kuma karon farko da Neymar ke naman lashe babbar kyautar a duniyar tamola.

Messi ne ya jagoranci Barcelona ga nasarar lashe kofuna uku a kakar da ta gabata, wadanda suka hada da kofin La liga da Copa del Ray da kuma kofin zakarun Turai, kuma a bana ana ganin ya fi Ronaldo kwarin guiwar lashe kyautar.

Ko da ya ke Ronaldo ke da yawan kwallaye a La liga tare da jefa kwallaye 7 a gasar zakarun Turai, amma babu wani kofi da ya lashe wa Real Madrid a kakar da ta gabata.

A bangaren Gwarzon Kociya.

Kocin Bayern Munich Pep Guardiola da na Barcelona Luis Enrique ke takarar gwarzon koci a bana tare da Dan Argentina Jorge Sampaoli, da ya jagoranci Chile ga nasarar lashe Copa America.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.