Isa ga babban shafi
Zakarun Turai

Zakarun Turai: Chelsea da Arsenal na da aiki a gabansu

Bayern Munich da Barcelona na iya samun makin da suke so domin tsallakawa zuwa zagaye na biyu a gasar zakatun Turai a yau Talata a yayin da Arsenal da Chelsea ke da jan aiki a gabansu.

Kocin Chelsea, Jose Mourinho.
Kocin Chelsea, Jose Mourinho. REUTERS
Talla

Roma ce ke bi ma Barcelona a teburin rukuninsu na E da maki 5, kuma tana iya ficewa gasar idan har ta gasa doke Barcelona kuma Bayer Leverkusen ta doke BATE Borisov ta Belarus.

Rukunin F: Arsenal da Dinamo Zagreb, Bayern Munich da Olympiakos

An shafe kaka 15 Arsenal na kai wa zagaye na biyu a gasar zakarun Turai, kuma a bana idan har tana son tsallakewa sai ta samu galaba akan Zagreb sannan idan tana iya rama kashi da ta sha a gun Olympiakos nan da makwanni biyu masu zuwa.

Amma idan Bayern Munich da Olympiakos suka tashi kunnen doki ko babu ci a yau Talata dukkaninsu sun tsallake zuwa zagaye na biyu.

Rukunin G: Porto da Dynamo Kiev, Chelsea da Maccabi Tel Aviv

Har yanzu ba a samu galabar Porto ba a rukuninsu na G, kuma a yau kungiyar na iya tsallakewa zuwa zagaye na biyu idan ta doke Dynamo Kiev.

Ko maki guda Porto ta samu ta tsallake amma sai idan Chelsea ta yi barin maki a karawarta da Maccabi Tel Aviv ta Isra’ila.

Chelsea ce dai a matsayi na biyu a teburinsu na G, kuma kungiyar na iya kai wa zagaye na biyu a yau idan har ta samu nasara akan Maccabi amma sai idan Dynamo ta kasa doke Porto.

Rukunin H: St Petersburg da Valencia, Lyon da Gent
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.