Platini na ci gaba da fuskantar tuhuma
An kaddamar da sabbin tambayoyi game da karban cin hancin Swiss France miliyan 2 da ake zargin shugaban hukumar kwallon kafa ta Turai Michel Platini da karban su ba bisa ka’ida ba daga hannun Sepp Blatter, jagoran hukumar FIFA.
Wallafawa ranar:
To sai dai har yanzu Platini ya jajirce kan cewa shi bai aikata wani laifi ba kuma zai tsaya takarar shugabancin hukumar kwallon kafa ta duniya.
A nata bangaren hukumar kwallon kafa ta kasar Ingila ta ce, ta na goyon bayan Platini dangane da neman kujerar shugabancin FIFA amma kuma ta goyi bayan a bincike shi game da wannan zargi na karban kudade ba bisa ka’ida ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu