Isa ga babban shafi
Wasanni

An haramtawa Warner shiga harkokin wasa

An haramta wa tsohon jami'in hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA, Jack Warner shiga harkokin kwallon kafa har iya tsawon rayuwarsa, wannna kuma ya biyo baya samun sa da Kwamitin da'a na Fifa, ya yi da hannu dumu-dumu a wata badakalar cin haci da ta shafi miliyoyin daloli.

Tsohon Maitaimakin shugaban FIFA Jack Warner
Tsohon Maitaimakin shugaban FIFA Jack Warner REUTERS/Andrea de Silva/
Talla

A shekara ta 2011 Jack ya yi murabus daga shugabancI hukumar bayan da aka soma zarginsa da hannu a ayyukan cuwa-cuwa.

Yanzu dai Wannan Matakin da aka dauka a kan Warner ya biyo bayan binciken da aka gudanar kan tsarin da aka bi wajen bai wa Rasha da Qatar damar daukar bakuncin gasar cin kofin duniya na shekarun 2018 da kuma 2022.

Baya ga wannan anyi kuma waiwaye kan harkokin da ya yi tun daga farkon Janairu bana inda aka gano wasu matsaloli da abubuwa da ya aiwatar da suka sabawa dokokin hukumar.

Tuni suma dai hukumomi a Amurka suka shiga binciken kan wannan zargin na cin hanci da hallata kudaden haramu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.