Isa ga babban shafi
Wasanni

Ibrahimovic ya zura kwallonsa na farko a wannan kaka

A Faransa karon farko tun buda kakar wasan Ligue 1 na bana, Zlatan Ibrahimovic ya zura kwallonsa na farko a raga, a karawar da aka yi tsakanin kulob dinsa na PSG da kuma Guingamp har ma aka tashi wasan ci 3 da nema PSG ce ta yi nasara.

PSG a karawarta da Guingamp
PSG a karawarta da Guingamp AFP
Talla

Kulob din PSG ya buga wasanni 7 a wannan kaka, kuma sai a jiya wanda ake kallo a matsayin gwarzo a wannan kulob wato Ibrahimovic ya zura kwallonsa na farko. Shi ma Angel Di Maria ya samu nasarar zura kwallo a raga a wannan wasa na jiya.

Yanzu haka dai PSG na ci gaba da jagorantar teburin gasar Ligue 1 ta Faransa a kakar bana, kuma wannan kulob ne ke rike da kofin gasar na kakar wasannin da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.