PSG zata taimaka wa 'yan gudun hijiran da suke tsallaka zuwa Turai
Kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint-Germain ko PSG, dake rike da kambin gasar Lig din Faransa tace zata bayar da gudunmawar kudi EURO miliyon 1, ga wasu kugiyoyi, ta hannun gidauniyar kungiyarta da aka kaddamar don taimaka wa ‘yan gudun hijiran dake kwarara zuwa kasashen Turai.
Wallafawa ranar:
Kungiyar zata yi haka ne don ganin ‘yan gudun hijirar sun sami sabuwar rayuwa a nahiyar Turai.
Wannan matakin da kungiyar ta dauka na zuwa ne bayan wasu manyan kungiyoyin na kwallon kafa a sassan duniya daban daban, kamr su Real Madrid ta Spain, Roma Italiya da Bayern Munich kasar Jamus, sun bayyana aniyar taimakawa ‘yan gudun hijiran, da akasarinsu suka fito daga kasar Syria, da yaki ya daidaita.
Yanzu haka dai kasashen na turai suna ci gaba da samar da hoyoyin karbar ‘yan gudun hijiran.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu