Isa ga babban shafi
wasanni

Yan gudun hijira 1000 zasu kalli wasan kwallo a Jamus

Kungiyar Kwallon kafar ta St. Pauli dake birnin Hamburg na Kasar Jamus ta gayyaci ‘Yan Gudun Hijira kimanin 1000 da aka baiwa mafaka a Kasar dasu halarci wasan sada zumunta da kuniyar zata yi da Borrussia Dortmund a ranar talata mai zuwa.

Dubban Yan gudun hijara ne ke neman mafaka a Kasashen Turai.
Dubban Yan gudun hijara ne ke neman mafaka a Kasashen Turai. REUTERS/Laszlo Balogh
Talla

Za’a dai gudanar da wasan ne a filiin wasa na Millerntor yayin da yan wasan Kungiyar zasu riko hannayen kananan yaran Yan gudun hijiran gabanin fara wasan.

Kungiyoyin kwallon kafa dai da dama a Kasar Jamus sun bayyana shirye shiryensu na tallafawa 'Yan gudun hijira dake kwarara cikin Kasar.

Kuma tuni Bayern Munich ta dau alwashin ware euro miliyan daya domin taimakawa musu sannan zata tanadi sansanin baiwa yan gudun hijira horo, inda kuma za’a dinga basu abinci tare da koyawa yaransu harshen Jamusanci.

A bangare guda, shima kwamitin shirye wasannin Olympic zai bada dalar Amurka biliyan biyu domin magance matsalar kwarrarar 'Yan gudun Hijra a nahiyar Turai kamar yadda shugaban kwamitin Thomas Bach ya sanar a yau jumma’a.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.