Isa ga babban shafi
wasanni

Joon ya zargi AFC da nuna goyon baya ga Platini

Dan takakar shugabancin hukumar kwalon kafa ta duniya daga Kasar Korea ta kudu, Chung Mong Joon ya caccaki hukumar kwallon kafa ta Asiya bisa nuna goyon bayanta ga abokin takarrasa Michel platini,inda ya ce hakan ya sabawa dokar hukumar FIFA. 

Chung Mong-Joon dan takarar shugabancin FIFA daga Kasar Korea ta kudu
Chung Mong-Joon dan takarar shugabancin FIFA daga Kasar Korea ta kudu REUTERS/Kim Hong-Ji
Talla

Mong-Joon ya bayyana cewa hukumar kwallon Asiya karkashin jagorancin Sheik Salman ta bayyana goyon bayan nata ne a fili ga Platini, inda kuma ta aike da wasiku ga mambobinta amma banda mambobinta na kasashen Korea ta kudu da kuma Jordan.

Kasar Jordan nada Yarima Ali Bin Hussain da shima zai tsaya takarar shugabancin hukumar ta FIFA.

Wannan wasikar na dauke da wani sashi inda mambobin zasu sanya hannu domin nuna goyon bayansu ga Platini, wanda a yanzu shine shugaban hukumar kwallon kafa ta Turai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.