Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Bale ya ci Tottenham

Gareth Bale ya zira kwallo a ragar tsohuwar kungiyar shi Tottenham inda Real Madrid ta samu nasara da ci 2-0 a wasan sada zumunci da suka buga a jiya Talata. Yanzu Real Madrid za ta hadu da Bayern Munich a wasan karshe na gasar lashe kofin Audi a Jamus.

Gareth Bale ya zira kwallo a ragar tsohuwar kungiyar shi Tottenham inda Real Madrid ta samu nasara da ci 2-0
Gareth Bale ya zira kwallo a ragar tsohuwar kungiyar shi Tottenham inda Real Madrid ta samu nasara da ci 2-0 Reuters
Talla

Wannan ne karon farko da Gareth Bale ya hadu da toshuwar kungiyar shi tun bayan komawarsa Real Madrid a 2013 a matsayin tsadadden dan wasan kwallon kafa a duniya.
Kusan dai Fam Miliyan 85 da rabi Real Madrid ta saye dan wasan daga Tottenham.

Bale ya jefa kwallon ne a raga ana minti 79 da soma wasa, bayan James Rodriguez ya fara zira kwallo a ragar Tottenham tun kafin aje hutun rabin lokaci.

Bayern Munich kuma ta lallasa AC Milan ne 3 da 0, kuma a yau Laraba ne Bayern za ta kara da Real Madrid domin lashe kofin Kamfanin Audi mai kera motoci da ake gudanarwa kafin soma kaka duk shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.