Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Madrid ta samu sa’ar Milan a Fanariti

Real Madrid ta samu sa’ar AC Milan ci 10 da 9 a bugun fanariti a wasan sada zumunci na share fagen soma kakar wasa da suka kara a jiya Alhamis a birnin Shanghai na kasar China.

Carlos Bacca na AC Milan na gumurzu da Sergio Ramos na Real Madrid a wasan share fagen kaka
Carlos Bacca na AC Milan na gumurzu da Sergio Ramos na Real Madrid a wasan share fagen kaka REUTERS/Aly Song
Talla

Matashin golan AC Milan dan shekaru 16 ne ya barar da da fanariti wanda ya ba Real Madrid nasara.

Manyan kungiyoyin biyu na Turai sun je bugun fanariti bayan kammala lokatan wasan minti 90 babu wanda ya zira kwallo a raga.

Kuma a bugun fanariti sai da dukkanin ‘yan wasan suka buga har ta kai ga masu tsaron gida.

Ronaldo da Gareth Bale dukkaninsu sun buga wasan amma babu wanda ya iya jefa kwallo a raga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.