Isa ga babban shafi
FIFA

Hukumar kwallon Asiya ta goyi bayan Platini

Hukumar da ke kula da kwallon kafa a yankin Asiya ta bayyana goyon bayanta ga Platini da ke neman shugabancin hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA.

Shugaban kwallon Turai Michel Platini ya shiga takarar shugabancin FIFA
Shugaban kwallon Turai Michel Platini ya shiga takarar shugabancin FIFA REUTERS/Olivier Pon/Files
Talla

Hakan ke nuna Platini ya fara samun goyon bayan hukumomin kwallo a sassan duniya a zaben FIFA da za a gudanar a ranar 26 ga watan Fabrairun badi.

A shekaran jiya ne dai Platini ya ce zai shiga takara shugabancin FIFA bayan shugaba mai ci na yanzu Sepp Blatter ya yi murabus.

Sai dai hukumar ta Asiya ta bayyana goyon bayanta ga Platini duk da kuma akwai dan takara Yariman Jordan Ali bin al Hussein daga yankin na Asiya da attajirin Korea ta kudu Chung Mong-Joon, da ke neman kujerar shugabancin FIFA.

Yanzu haka kuma Hukumar kwallon Brazil ta bayyana goyon bayanta ga tsohon dan wasan kasar Zico wanda ke neman shiga takarar shugabancin hukumar FIFA.

Wannan matakin kuma ya kara wa Zico kwarin guiwa wanda ya dade yana neman amincewar hukumar kwallon Brazil domin mara masa baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.