Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Di Maria na daf da komawa PSG

Rahotanni na tabbatar da cewa dan wasan Manchester United Di Maria na daf da komawa Paris Saint Germain a Faransa bayan ya shafe shekara guda yana taka kwllo a Old Trafford a Ingila.

Angel Di Maria sanye da rigar Argentina
Angel Di Maria sanye da rigar Argentina AFP PHOTO / YURI CORTEZ
Talla

Alamun ficewar dan wasan Manchester United ya fito fili bayan ya ki bin tawagar kungiyar zuwa wasannin share fagen kaka a Amurka.

Kocin Manchester United Luis Van Gaal ya tabbatar wa manema labarai bayan ‘yan wasansa sun doke Barcelona a Amurka cewa Di Maria ya kauracewa tawagarsa a wasannin share fagen kaka.

Kodayake an ba dan wasan hutu da wani dan lokacin domin ya huta saboda gasar Copa America da ya fafata a watan jiya.

Kocin PSG Laurent Blanc ta tattabar da bukatar shi akan Di Maria tare da cewa suna kan tattaunawa da Man United domin mallakar dan wasan.

A bara ne Di Maria ya koma Manchester United daga Real Madrid akan kudi kusan fam miliyan 60.

Kuma yanzu Jaridun Faransa sun ruwaito cewa PSG zata zuba kudi kimanin euro Miliyan 63 domin karbo Di Maria daga Manchester United.

PSG ta dade tana son karbo Di Maria tun kafin komawarsa Manchester United.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.