An sace tubalin da Messi ya aza a filin wasanni na Gabon
An sace tubulin da Lionel Messi na Argentina ya aza a filin wasannin da Kasar Gabon ke gina wa saboda daukan bakwancin gasar cin kofin nahiyar Afrika a shekara ta 2017.
Wallafawa ranar:
Shugaban kasar ta Gabon Ali Bongo Ondimba ya gayyaci Lionel Messi domin ya aza wannan tubulin na ginin katafaran filin wasanni dake yankin Port Gentil a ranar asabar din data gabata.
Jim kadan da sace tubulin hukumomin kasar sun kira jami’an tsaro domin su bada cikakkun bayanai kan yadda lamarin ya faru.
A bangare guda, ziyarar Messi ta haifar da cece kuce a kasar inda aka zargi gwamantin Gabon da bashi kudade har Euro miliyan 3 da rabi domin ya kawo ziyarar yayin da al-ummar kasar ke fama da kunci na rayuwa.
To sai dai fadar Shugaban Kasar ta musanta wannan zargin.
Kuma wasu na ganin irin shigar da Messi ya yi a lokacin ziyarar kamar ya nuna kaskanci ne ga mutanen Afrika inda ya sanya gajeren wando da wata karamar farar riga da zane a jikinsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu