Isa ga babban shafi
Gabon

Shugaban Gabon ya musanta zargin ya ba Messi kudi

Fadar shugaban kasar Gabon ta musanta zargin da ke cewa an bai wa dan wasan kwallon kafa na kasar Argentina Lionel Messi wasu makudan kudade a ziyarar da ya kai a kasar.

Messi ya aza tubalin gina katafaren filin wasan kwallon kafa a Gabon
Messi ya aza tubalin gina katafaren filin wasan kwallon kafa a Gabon REUTERS/Gérauds Wilfried Obangome
Talla

A cikin makon da ya gabata ne dai shugaban Ali Bango Ndimba ya gayyaci Messi zuwa kasar, yayin da wasu ‘yan siyasa da kuma masu adawa da gwamnatin ke zargin cewa an bai wa dan wasan na Barcelona makudan kudade.

Ziyarar Messi dai ta janyo cece-kuce a kasar, musamman a dandalayen sada zumunta na Intanet inda wasu mutanen Gabon ke ganin an kashe makudan kudade don tarbar Messi yayin da al’ummar kasar ke fama da kunci na rayuwa.

Wata mujallar wasanni a Faransa ce dai ta kara hura wutar kace-nace din kan labarin Messi ya karbi kudi da suka kai yuru miliyan uku da rabi.

Shugaban Gabon ne dai da kansa ya tuka Messi yana gefe a gaban jama’ar kasar a birnin Libreville.

Kuma wasu na ganin irin shigar da Messi ya yi a lokacin ziyarar kamar ya nuna kaskanci ne ga mutanen Afrika inda ya sanya gajeren wando da wata karamar farar riga da zane a jikinsa.

Messi dai ya kawo ziyara a Gabon ne domin aza tubalin gina katafaren filin wasan kwallon kafa a shirye shoryen da kasar ke yi don karbar bakuncin gasar cin kofin Afrika a 2017.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.