Isa ga babban shafi
Canada 2015

‘Yan Matan Amurka sun lashe kofin duniya

‘Yan matan Amurka sun lashe kofin duniya bayan sun lallasa ‘Yan matan Japan 5 da 2 a wasan karshe da suka fafata a gasar da aka gudanar a kasar Canada.

Sau uku 'Yan Matan Amurka na lashe kofin duniya.
Sau uku 'Yan Matan Amurka na lashe kofin duniya. REUTERS
Talla

Kwallaye uku Carli Lloyd ta jefa a raga, wacce ta kasance mace ta farko da ta jefa kwallaye uku a wasan karshe a gasar cin kofin duniya ta mata.

Carli Lloyd kuma ta karbi takalmin zinari a matsayin jarumar ‘yar wasa a gasar, yayin da golan Japan ta karbi safar hannun zinari ta masu tsaron gida.

Sau uku ke nan ‘yan matan Amurka na lashe kofin, bayan sun doke ‘Yan matan Japan da suka lashe kofin a baya.

Rahotanni sun ce mutanen Japan da dama sun kwankwadi barasa domin nuna rashin jin dadin duka da matan kasar suka sha a hannun ‘Yan matan Amurka.

‘Yan matan Amurka dai sun rama kashin da suka sha ne a hannun Matan Japan a 2011.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.