UEFA na tattauna hanyar rage kudadden da Kulob din Turai ke kashe wa
Hukumar kwallon kafar Nahiyar Turai UEFA, ta fara wani zaman tattaunawa domin samar da haske a kan yadda Kulob din Turai ke kashe kudadensu.Tsarin da hukumar ke fatan gani an samu sauyi a kai karkashin jagoranci shugabanta Micheal Platini zai taimakawa kungiyoyi da dama.
Wallafawa ranar:
Idan aka cimma matsaya Kungiyoyin irinsu Manchester city da Paris saint Germain PSG wanda suka fi kowani kungiya kwallon kafa, kashe kudi a turai za su rage adaddin kudadden da suke karkashe wa.
Platini dai ya jima yana alkawarin samar da sauyi a harkan kwallon kafar turai, wanda shine baban batu da yake fatan ya samar da sauyi a kai.
Yanzu dai haka akwai Kungiyoyin kwallayen kafa 14 a turai da ake son tsarin ya fara aiki a kan su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu