Amnesty ta bukaci FIFA ta shiga tsakani.
A cikin rahoton da Amnesty ta fitar ta bayyana damuwa akan yadda ake cin zarafin lebarori a Qatar na rashin biyansu kudaden da suka dace, tare da hanawa masu ficewa kasar.
Sai dai kuma kamfanonin da ke hulda da hukumar FIFA Coca Cola da kamfanin hada hadar kudi na Visa sun ce za su taimaka tare da matsa kaimi ga hukumar FIFA domin shiga tsakanin rikicin lebarori a Qatar.