Isa ga babban shafi
Zakarun Turai

Juventus za ta hadu da Barcelona a Berlin

Kungiyar juventus ta tsallake zuwa zagayen karshe a gasar zakarun Turai bayan ta doke Real Madrid da jimillar kwallaye 3 da 2 a wasan dab da na karshe a fafatawar da suka yi jiya Laraba. Alvaro Morata ne ya taimakawa Juve rike Madrid 1 da 1, wanda ya farke kwallon da Cristiano Ronaldo ya fara jefawa a raga a bugun fanariti.

Juventus za ta hadu da Barcelona a Berlin bayan ta yi waje da Real Madrid a gasar zakarun Turai
Juventus za ta hadu da Barcelona a Berlin bayan ta yi waje da Real Madrid a gasar zakarun Turai Reuters / Sergio Perez
Talla

Yanzu Juve za ta hadu ne da Barcelona a wasan karshe da za su fafata a ranar 6 ga watan gobe a birnin Berlin na Jamus.

Haduwar Barcelona da Juventus dai karabkiya ce za a yi tsakanin Luis Suarez da Giorgio Chiellini, wanda Suarez ya dankarawa cizo a gasar cin kofin duniya a Brazil, lamarin da ya sa aka dakatar da shi buga kwallo na tsawon watanni hudu.

Haka kuma Suarez zai hadu da Patrice Evra, na Faransa wanda Suarez ya nuna wa wariyar launin fata a lokacin da suke taka kwallo a Liverpool da Manchester United.

Bayan kammala wasan jiya dai Evra yace zai gaisa da Suarez idan sun hadu.
A lokacin an dakatar da Suarez na tsawon wasanni 8 saboda laifin nunawa Evra wariya.

MAKOMAR ANCELOTTI

Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya ce shi ba zai iya tantance makomarsa ba a kungiyar a kaka mai zuwa bayan Juventus ta kore su a gasar zakarun Turai.

Alamu dai na tabbatar da cewa Real Madrid za a kammala kaka ba tare da ta lashe kofi ba, yayin da Barcelona ke jan ragamar teburin La liga da maki 4, sannan ita ce za ta buga wasan karshe da Bilbao a gaar Copa del Ray.

Wasu Jaridun Spain sun yi sharhi akan cewa yana da wahala Ancelotti ya ci gaba da horar da Real Madrid.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.