Isa ga babban shafi
wasanni

Juventus na burin dawowar Pogba cikin kankanin lokaci

Kungiyar Juventus na burin cewa dan wasanta Paul Pogba zai dawo daga jinya cikin kankanin loakaci, domin samun damar haskawa da Real Madrid a gasar zakarun Turai

Paul Pogba na Juventus
Paul Pogba na Juventus REUTERS/Ueslei Marcelino
Talla

Juventus da Real Madrid za su fafata ne a wasan zagaye na biyu kusa wasan dab da na karshe a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai ranar talata mai zuwa.

Kocin Klub din na Juventus Massimiliano Allegri ya bayyana cewa, binciken lafiyar Pogba ya nuna cewa da sauki kuma suna sa ran zai warke da wur wuri kuma zai buga wannan karawar da Real Madrid.

Pogba mai shekaru 22, ya shafe kimanin wata daya da rabi yana jinya tun bayan da ya samu rauni a cinyarsa a wasan da suka kara da Boarrussia Dortmun a watan Maris a gasar zakarun Turai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.