Isa ga babban shafi
Europa League

An hada Napoli da Dnipro, Sevilla da Fiorentina

An hada Napoli  wasa da Dnipro Dnipropetrovsk, yayin da kuma aka hada Sevilla da Fiorentina a zagayen kusa da da karshe a gasar Europa League da aka gudanar a hedikwatar hukumar kwallon Turai a birnin Nyon.

'Yan wasan Sevilla suna murnan lashe kofin Europa League bayan sun doke Benfica
'Yan wasan Sevilla suna murnan lashe kofin Europa League bayan sun doke Benfica REUTERS/Albert Gea
Talla

Sevilla mai rike da kofin gasar ta tsallake zuwa zagayen dab da na karshe a jiya Alhamis bayan ta doke Zenit St Petersburg da jimillar kwallaye 4 da 3.

Haka kuma kungiyoyin Italiya guda biyu Fiorentina, Napoli sun tsallake zuwa zagayen dab da na karshe bayan sun samu nasara a wasanninsu na jiya

Fiorentina ta yi waje da da Dynamo Kiev ci 2 da 0, yayin da kuma Napoli ta yi waje da Wolfsburg da jimillar kwallaye 6 da 3.

Wannan ne karon farko da kungiyar Dnipro ta Ukraine ta tsallake zuwa zagayen dab da na karshe a tarihin Europa leadue bayan ta doke Club Brugge ci 1-0.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.